✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 4 sun tsere daga gidan yarin ISWAP

Mutanen sun tsere ne bayan an yi kaca-kaca da gidan yarin ISWAP a wata musayar wuta tsakanin kungiyar da Boko Haram.

Akalla mutum hudu da ISWAP ta yi garkuwa da su a hanyar Maiduguri zuwa Gajiram a Jihar Borno sun tsere daga gidan yarin kungiyar.

Mutanen sun tsere ne bayan an yi kaca-kaca da gidan yarin ISWAP a wata musayar wuta tsakanin kungiyar da Boko Haram.

Mutanen da suka tsere ranar Juma’a da dare daga gidan yarin da ke Tumbum Allura da Kangara da ke yankin Abadam, sun fada hannun ISWAP ne tun ranar 3 ga watan Agusta, 2022.

Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zagazola Makama, kwararre kan yaki da ta’addanci kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Tafkin Chadi, cewa fursunonin sun tsere ne zuwa daya daga cikin kasashen da ke makwabtaka da Najeriya ta cikin daji.

Majiyar ta kara da  cewa za a mika mutanen ga hukuma domin ci gaba da lura da su.

Myakan Boko Haram da ke karkashin Abu Ummah ko Bakoura Doro da wasu kwamandoji hudu sun kai hari a sansanonin ISWAP da ke Tumbum Allura da Kangar a Arewa maso Gabashin Abadam a Jihar Borno.

Rikicin wanda ya faro da misalin karfe 4 na yammacin ranar Juma’a ya kai har zuwa karfe 5 na asubahin ranar Asabar, inda bangarorin suka kashe wa juna mayaka da dama.