✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 5 sun nitse a ruwa suna kokarin tsere wa ’yan bindiga a kauyen Abuja

Mutanen sun hada da maza hudu da matar aure daya

Mutum biyar sun nitse a ruwa a kokarinsu na tsere wa harin ’yan bindiga a kauyen Chakumi da ke gundumar Gurdi a yankin Babban Birnin Tarayya Abuja.

Mutanen, wadanda suka hada da maza hudu da matar aure daya sun gamu da ajalin nasu ne a kogin Gurara da ke kusa da yankin, cikin karamar hukumar Gwagwalada.

Dagacin garin na Chakumi, Mohammed Magaji ne ya tabbatar wa Aminiya faruwar iftila’in wanda ya ce ya faru ne wajen karfe 11:00 na ranar Laraba.

Ya ce mutanen sun tsaka da aiki a gonakinsu ne lokacin da suka ga ’yan bindigar na kokarin kai musu harin.

Dagacin ya ce ganin haka ne ya sa suka bazama suka tafi domin hawa jirgin don tserewa zuwa kauyen Daku mai makwabtaka da su, amma jirgin ya kife a kogin Gurara da su.

“Maganar da nake yi da kai yanzu haka ko gawarwkinsu ba a gano ba, yayin da masunta daga garina da kuma kauyen Daku ke ci gaba da lalubensu,” inji basaraken.

Mohammed Magaji, wanda ya koka kan ayyukan ’yan bindiga a yankin, ya ce a yanzu manoma ba sa iya zuwa gonakinsu saboda fargabar masu garkuwa da mutane.

Shi ma Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Abaji, Ibrahim Abubakar, ya tabbatar ya faruwar lamarin, inda ya ce a cikin mutanen har da dan uwansa.

“Akwai dan uwana ma a cikin wadanda suka nitse, kuma maganar da nake da kai yanzu haka ba a kai ga gano gawarwkinsu ba,” inji shi.

Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sanda shiyyar Abuja, DSP Adeh Josephine, ba ta amsa sakon kar-ta-kwanan da ya aike mata ba kan lamarin har zuwa lokacin hada wannan rahoton.