✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 8 sun sake nitsewa a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa

Wannan dai shi ne karo na biyu da aka sami hatsarin a yankin

Akalla mutum takwas ne suka mutu sakamakon nitsewar jirgin ruwa da ya auku a kogin Oyoma kusa da Oporoma a Karamar Hukumar Ijaw ta Kudu a Jihar Bayelsa.

Hatsarin ya auku ne a ranar Larabar da ta gabata, kasa da mako daya da faruwar makamancin hakan inda wasu mutum shida suka kwanta dama, duk dai cikin yankin guda.

An ce hatsarin ya auku ne tsakanin jiragen ruwa biyu saboda rashin kyawun yanayi sakamakon ruwan saman da aka ce ana yi a lokacin da hatsarin ya auku.

Bayanai sun ce daya daga cikin jiragen na dauke da fasinjoji 12 da ya kwaso su daga Korokorosei zuwa Ayama, yayin da gudan ke dauke da kayan abinci bayan da ya taso daga Yenagoa zai tafi Ayama.

Wata majiya ta ce duk da ganin yanayin da kogin ya kawo sakamakon ruwan sama, wannan bai sa matafiyan yin amfani da rigar kariya (life jacket) ba.

Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Jirgin Ruwa (MWUN) na yankin, Ipigansi Ogoniba, ya tabbatar da aukuwar hatsarin, inda ya ce, saba wa doka ne daukar fasinja ba tare da sanya rigar kariya ba.

Haka shi ma Kakakin ’Yan Sandan Jihar Bayelsa, Asinim Butswat, ya tabbatar da faruwar ibtila’in.