✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutumin da ya yi wa uwa fyade a gaban ’yarta ya shiga hannu

’Yan Sibil Difens sun cafke shi bayan wata bakwai yana buya bayan ya aikata ta'asar

Jami’an Sibil Difens sun cafke wani mutum mai shekaru 47 kan zargi yi wa wata mata  fyade a gaban ’yarta mai shekaru biyu.

Kakakin Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) reshen Jihar Kwara, Ayeni Olasunkanmi, ya ce tun a watan Yunin 2022 hukumar ke farautar sa, amma sai a ranar 5 ga watan Janairu ta cafke shi a garin Makwa na jihar Neja, inda ya buya.

“Bayan mun kama shi, ya fada mana cewa ya haura gidan matar ce lokacin babu kowa, daga ita sai ’yarta mai shekaru biyu kuma a gaban ’yar ya yi wa uwar fyaden ya kuma sace mata kwamfutoci biyu da wayoyin ta biyu da yayi”, in ji Olasunkanmi.

Ya ce har yanzu dai hukumar na farutar wadanda suka sayi kayan daga hannunsa, sannan ya jan hankalin mutane su rika lura da wadanda suke sayen kaya a hannunsu.

Haka kuma ya ce za su gurfanar da mutumin a gaban kotu, domin ya girbi abin da ya shuka.