Na kagara na bar mulkin Najeriya – Buhari | Aminiya

Na kagara na bar mulkin Najeriya – Buhari

Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari
    Muideen Olaniyi da Sani Ibrahim Paki

Shugaban Najeriya Muhammadu buhari ya ce ya kagara ya mika ragamar mulkin kasar ga wanda zai gaje shi saboda wahalar mulkin da yake sha.

Ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin wasu Gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki da wasu ’yan majalisa lokacin da suka kai masa ziyarar Sallah a gidansa da ke Daura a Jihar Katsina ranar Litinin.

A ranar Juma’a ce Shugaban ya tafi garin na Daura domin gudanar da bukukuwan Sallar Layya ta bana.

Ya kuma ja hankalin bakin nasa da su yi taka-tsan-tsan da masu neman taimako a wajensu.

“Nan da badi warhaka, wa’adin mulkina na shekara takwas ya zo karshe,” inji shi.

Buhari ya kuma shaida musu cewa kusan tsawon shekara guda ke nan bai ziyarci gidan nasa na Daura ba saboda yanayin ayyuka.

Sai dai ya ce da zarar wa’adin mulkin nasa ya kare, a Daurar zai koma ya tare ba a Kaduna ba.

Ya kuma ce yana yi wa duk wanda zai gaje shi a 2023 fatan alheri.

Dangane da batun tsaro kuwa, Shugaban ya ce duk da shiyyar Arewa maso Yamma ta zo da sabbin kalubale, gwamnatinsa ta sami gagarumar nasara a Arewa maso Gabas da Kudu maso Kudu.

“Na kagara na tafi. A zahirin gaskiya mulkin nan babu sauki ko daya. Amma ina godiya ga Allah cewa mutane suna godewa irin sadaukarwar da muke yi musu,” inji shi.