✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Na shekara 50 ina sana’ar figar kaji’

Ya ce yana da wahala mai sana’ar figar kaji ya rasa na cefane

Malam Garba Adamu dattijo ne da ke sana’ar figar kaji a Maiduguri, inda ya ce ya shafe kusan shekara 50 yana wannan sana’a. A zantawarsa da Aminiya ya bayyana rufin asirin da ke cikin sana’ar da fadi-tashin rayuwa da ya yi fama da shi.

Yaushe ka fara sana’ar figar kaji?

Na fara wannan sana’a ta gyaran kaji tun a 1973. Ka ga yau shekara 50 ke nan, kuma na zo nan Maiduguri ne tun a 1962, domin yin karatun allo. Kuma babu wanda ya koya min wannan sana’a, na ga a wancan lokaci babu wani mai yin ta ne, sai na ga ya dace in yi wani abu da zai taimaka min wajen ci gaban rayuwa da samun abin kashewa.

Duk da ka san mafi yawan almajirai a nan Maiduguri ba ma yin bara, to sai ya kasance idan na tashi daga karatun allo sai in tafi wurin yin figar kaji. A haka
na fara sannu a hankali har wasu suka zo suka fara koyo.

Akwai wadanda ka koya wa sana’ar zuwa yanzu?

Na koya wa mutane da yawa da su ma suka mai da ta babbar sana’ar da suke yi, wasu suna nan Maiduguri, wasu suna Kano wasu na Abuja, kai kusan ko’ina a kasar nan ina da wadanda na koya wa
wannan sana’a.

Suna da yawa ba zan iya tuna adadinsu ba, amma dai na san na koya wa mutane masu yawan gaske, domin kamar yadda na fada maka ni ne mutum na farko da ya fara yin irin wannan sana’a a nan
cikin garin Maiduguri.

Saboda yawan yaran da suka koyi sana’ar, akasarin lokaci sai dai in ga mutum ya zo ya gaishe ni, ya ce shi ne wane da ya koyi sana’a a wajena. Akwai wadanda suka yi kudi a dalilin wannan sana’a, wasu kuma suna sayar da kajin da kiwon su.

Wane rufin asiri ne a cikinta da kuma kalubale?

Ka ga sana’ar nan da ita na yi aure nake rike da iyalina, na aurar da ’ya’ya da yawa, kuma ina daukar nauyin karatun yarana da taimaka wa jama’a. A yanzu haka ina da ’ya’ya kusan 20 kuma da yawansu sun yi aure duk ta hanyar wannan sana’a.

Ina kuma rike da sauran ’yan uwa duk da sana’ar nake biya musu kudin makaranta muke rufa wa kanmu asiri.

Sannan batun kalubale akwai shi domin wani lokaci mutum zai kawo kajinsa a gyara, amma sai wani ya karba a matsayin nasa, mun sha samun irin haka karshe dai dole sai mun biya, wani kuma ya yafe.

Idan aka kwatanta da shekarun baya za a iya cewa sana’ar ta fi yanzu ganin a wancan lokaci kusan kai kadai ne ke yin ta. Yaya lamarin yake a yanzu ganin kuna da yawa?

Ai ita wannan sana’a kamar yadda na fada maka a baya Allah Ya sa albarka a cikinta, kusan duk wanda ka gani a nan yana wannan sana’a cikin daya ne ko biyu. Ko dai a nan ya koya ko kuma namu ne, kuma idan ka duba a yanzu an fi sayen kajin, to ka ga babu abin da za mu ce sai godiya ga Allah, domin duk abin da sana’a take wa mutum ta yi mana.

Ganin karamar sana’a ce masu manyan sana’o’i suna iya fitowa wata rana su rasa na cefene. Shin hakan takan faru da kai?

Gaskiya yana da wahala a ce mun fito mun tashi ba a samu abin yin cefane ba. Sai dai ka san yanayi na rayuwa, wata rana a samu da yawa wata rana kadan.
Haka da ma rayuwar take don wani lokacin za ka iya gyara kaji sama da 100, amma wani lokaci sai ka ga da kyar a samu goma, domin ko manyan ’yan kasuwa sukan iya fitowa ka ga ba su yi ciniki ba. Sai dai ka san sana’ar hannu ba kamar kasuwanci ba ne. Da wuya dai a fito a ce an rasa yadda za a yi da ikon
Allah ana samun abin da za a sa a bakin salati.

Wane kira kake da shi ga matasa masu zaman banza?

Zaman kashe wando ba abu
ba ne mai kyau, dole ne matasa su tashi tsaye su kama sana’a kada a zauna a majalisa, wannan zamanin ya wuce. Kamata ya yi kowa ya tashi ya kama sana’a, domin zaman banza ba ya da kyau. Duk wanda ya tashi Allah zai taimake shi. Komai kankantar sana’a, a tashi a yi ta, akwai samu a cikinta idan kuwa mutum ya kashe zuciya abokin
shawararsa Shaidan ne, wanda zai jefa shi ga halaka.

Wane kira kake da shi ga gwamnati?

Kirana a taimaka mana, mu masu karamar sana’a don inganta sana’ar, saboda da ita muke gudanar da komai na rayuwarmu ba tare mun kashe zuciya ba.

Da fatar gwamnatin jiha da ta karamar hukuma za su ji mu. Su taimaka mana do dada bunkasa sana’armu ta yadda za mu hada da kasuwancin kajin.