✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAJERIYA A YAU: Wa Ke Da Ikon Dakatar Da Ganduje A APC?

Shin su waye mutanen da suka dakatar da Ganduje daga jam’iyyar APC a matakin mazaba?

More Podcasts

An shiga saƙe-saƙe game da mutanen da suka yi ikirarin dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Ganduje, a mazabarsa.

Sai dai uwar jam’iyyar ta yi watsi da hakan, inda kuma daga bisani suka zargi jami’iyyar adawa da daukar nauyin wadanda suka yi ungulu da kan zabon.

To amma ko da a ce za a dauki irin wannan matakin, wa ke da hurumin dakatar da shugaban jam’iyyar ta APC na kasa a doka? Shirin Najeriya a Yau na da karin bayani.

Domin sauke cikakken shirin, latsa nan