✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NAJERIYA A YAU: Yadda Matasa Za Su Mori Tsare-Tsaren Bayar Da Bashi

Hanyoyi masu sauki na samun bashi domin farar sana'a a Najeriya

More Podcasts

Domin sauke shirin latsa nan

Matasa da dama na fama da rashin sanin hanyoyin samun bashi domin fara sana’a.

A ’yan shekarun nan, gwamnatin Najeriya ta fitar da tsare-tsare bayar da bashi ga manoma da masu kanana da matsakaitan sana’o’i da dangoginsu; sai dai kuma yawancin matasan kasar ba su san hanyar da za su bi domin samu bashin ba, wasu kuma su ce in ma sun nema ba sa samu.

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya binciko hanyoyin da mai bukatar bashi domin fara sana’a zai bi, ya kuma samu a cikin sauki.