Najeriya A Yau: Yadda uba ya yi wa ’yarsa fyade har ta samu ciki | Aminiya

Najeriya A Yau: Yadda uba ya yi wa ’yarsa fyade har ta samu ciki

Wata yarinya da ta yi zargin mahaifinta na yi mata fyade.
Wata yarinya da ta yi zargin mahaifinta na yi mata fyade.
    Muhammad Auwal Suleiman da Halima Djimrao

Domin sauke shirin latsa nan


Kunnuwan ’yan Najeriya sun jima sunajin kalmar fyade, amma labarin mahaifi ya yi wa ’yarsa fyade har ta samu ciki na iya zama sabon labari ga masu sauraro.

A karshen satin da ya gabata kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International sun ruwaito cewa a shekarar da ta gabata a kullum ana yi wa mata 374 fyade a Najeriya.

Shirin namu na yau na tafe da labarin daya daga cikin wadanda aka yi wa fyaden, sannan ya bankado me ke sa shari’ar fyade tafiyar hawainiya.

Najeriya A Yau: Shin fitar da ’yan Najeriya Kasashen waje aiki zai taimake ta?

Najeriya A Yau: Yadda Ake Taimakon Wanda Wuta Ta Kona