✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya: Matsala jiya, matsala yau kuma matsala gobe?

Shin bai kamata a samu jarumin mazan da ya kamata ya kwato ki daga kangin matsala zuwa sa’ida ba?

Tun bayan samun mulkin kai Najeriya ta fara shiga tsomomuwa, musamman wajen tafiyar da al’amuran mulki.

Allah dai Ya wadata kasar nan da dinbin arziki iri-iri kuma Ya wadata ta da yawan al’umma abin alfahari. Sai dai kash, an samu tasgaro wajen al’amuran mulki da gudanarwa.

A yau Gizago A yau Gizago (08065576011), nazari ya yi kan al’amarin, sannan ya karkare da tambayar cewa, shin haka za mu ci gaba da tafiya? A ce kasa ta kasance jiya matsala, yau matsala kuma gobe matsala?

Najeriya, haba kasata Najeriya! Shin wai haka al’amura za su ci gaba da kasancewa?

A ce jiya kina cikin matsala, yau kina cikin matsala kuma gobe ma ki ce za ki kasance cikin matsala?

Shin bai kamata a samu jarumin mazan da ya kamata ya kwato ki daga kangin matsala zuwa sa’ida ba?

Lallai kam ya dace al’ummar Najeriya, a wannan karon su hada hannu, su gano dalilan da suka sanya uwarsu (Najeriya) ta samu kanta cikin wannan mummunan yanayi, sannan su dauki haramar ceto ta daga ciki, yadda tun da jiya da yau tana cikin matsala, gobe ta samu waraka, ta samu sa’ida.

Ni kuwa na ce idan muka koma baya muka waiwayi tarihi, za mu ga yadda aka yi kasarmu Najeriya ta samu kanta cikin wannan karkataccen yanayi mai matukar muni.

Mu duba yadda Turawa suka mulke mu na tsawon lokaci, sannan suka zo suka damka wa al’ummarmu mulki a hannunsu a shekarar 1960.

Daga nan ne, duk da cewa an samu shugabanni adalai, masu kishin kasa da kishin al’ummarsu amma wasu munanan halaye da dabi’u suka gitto, suka yi mana karan-tsaye.

Farkon matsalolin da suka baibaye Najeriya a jiya, su ne ‘Kabilanci, Addinanci da Bangaranci.’

Kada ka raba daya biyu, wadannan ne tubalan matsalolin da suka yi wa kasarmu katutu a lokacin.

An samu rashin jituwa tsakanin al’ummun Kudanci da Arewaci, wanda babu shakka dalili ke nan ta kai mu ga yakar juna ta bangarori dabandaban na rayuwa.

Wadannan matsaloli, su ne suka haddasa har aka kashe wasu hazikan shugabanni da sunan juyin mulki.

An kashe muhimman mutane, adalan shugabanni ’yan Arewa, musamman ma su Sardaunan Sakkwato, Firimiyan Arewa, Sa Ahmadu Bello, an kashe Firaministan Najeriya na farko, Alhaji (Sa) Abubakar Tafawa Balewa da sauransu.

Har ila yau, wadannan matsaloli dai su ne kuma suka zama haddasuna, suka assasa mana yakin basasa, wanda aka fafata tsakanin 1967 zuwa 1970, inda aka yi asarar rayuwa da dinbin dukiya.

Wata babbar asara da aka yi ita ce ta haifar da rashin jituwa tsakanin al’ummun kasar nan.

Tun daga lokacin nan, har zuwa yau din nan da nake rubuta wannan tsokaci, wadannan matsaloli, na kabilanci, addinanci da bangaranci su ne ke taka mummunar rawa wajen haifar da munanan matsaloli a kasar nan kuma su ne suka sanya kasar ta tsaya cik, ba ta wani motsi na son barka.

Ta fannin kabilanci, a yanzu a kasar nan, duk inda mutum ya shiga, abu na farko da za a fara kallo shi ne kabilarsa.

Idan ba dolen dole ba, babu yadda za a yi Bahaushe ya yi tasiri a idanun Bayarabe, ko kuma Ibo ya yi tasiri a idanun Bafulatani ko kuma Bahaushe ya yi tasiri a idanun ’yan kabilar Ijaw. Wanda ba haka ya kamata a zauna ba.

Bambance-bambancen addini

Ta fannin addinanci kuwa, al’amarin ya yi matukar muni, ta yadda za ka ga mutane suna addini daya amma bambancin akida ta raba su.

Ke nan, bambance-bambancen addini da akida sun wuce yadda mutum ke zato.

Bambanci da rashin fahimtar juna tsakanin mabiyan addinan Musulunci da Kiristanci sun zama gagarabadau tsakanin al’umma.

Wannan kuwa ya haifar da rigingimu da yawa, babba daga cikinsu shi ne matsalar Boko Haram da ta ki ci ta ki cinyewa.

Ga mummunar aika-aikar ’yan bindigar daji da a kullum suke kashe al’umma da kona dukiyarsu da yi wa mata fyade, kamar kuma yadda suke yin garkuwa da mutane suna amsar kudin fansa.

Sanadiyyar wannan, an yi asarar rayuka fiye da kidaya, an yi asarar dukiya marar adadi, a yayin da kuma a yanzu haka dimbin mutane, maza da mata, yara da manya suna zaman tammaha a sansanonin gudun hijira, a yayin da mata da yawa da aka sace har yanzu ba amonsu balle labari.

Matslar bangaranci

Idan muka karkata zuwa ga matsalar da bangaranci ya haifar kuwa, labarin ba ya da dadin ji.

Domin kuwa al’amura sun koma suna tafiya ne bisa bangaranci. Harkar zabe, harkar aikin gwamnati, harkar auratayya da sauran dukkan lamurra sun zama idan ba daga yankinku mutum ya fito ba, sai ya samu matsala.

An samu lokacin da a Kudancin Najeriya, ana tilasta wa ’yan Arewa yankar takardar izinin zama can.

Ke nan dan Arewa ya zama bare a kasarsa ta haihuwa, wanda ba haka tsarin mulkin Najeriya ya nuna ba.

A ka’ida, dan Najeriya na da iko da ’yancin zabar duk inda zai zauna ya yi rayuwa ba tare da hantara ko tsangwama ba amma a yau bangaranci ya dakushe komai.

Satar dukiyar al’umma

Ya zama dole a samo maganin wadannan matsaloli, madamar ana son Najeriya ta yi kyau a gobe, madamar ana son a hana ci gaban matsaloli a rayuwar dan Najeriya makamantan wadanda suka faru a jiya kuma suke faruwa a yau.

Wata babbar matsala kuma ita ce ta bangaren almundahana, satar dukiyar gwamnati, kashemu-raba, cin hanci da rashawa, fashi da makami, satar mutane domin kudin fansa da sauran munanan al’amura.

A Najeriya, an fi ba dukiya da mallakarta muhimmanci fiye da ilimi.

Shugabanni sun mayar da dukiyar gwamnati kamar gadon gidansu.

Wannan yanayi ya haifar da tabarbarewar komai, babu ingantaccen tsarin koyo da koyarwa a makarantu – ilimi ya tabarbare.

Babu wutar lantarki, babu ingantattun asibitoci, babu, babu, babu… Kuma wannan matsala ta satar dukiyar gwamnati, ita ce ma babbar illar da ta ta’azzara ko kuma ta haifar da sauran matsaloli.

Yanzu mutum zai zama Gwamna bai da komai, amma kafin ya sauka ya mallaki manyan gidaje, ya mallaki asusun ajiya a kasashen waje.

A fili take yadda a yanzu ake ta bincike, inda za ka ji an ce wane tsohon Gwamna ya boye miliyan kaza ko Minista wane ya murkushe biliyan kaza, abin kamar almara.

Shin a haka za adawwama?

Shin anya haka za a ci gaba a kasar nan, matsala jiya, matsala yau kuma matsala gobe? Ni kuwa na ce allambaran ba ta sabuwa, bindiga a ruwa.

Ya zama dole talakawa su farka daga barci, ya dace malaman addini da malaman zamani su mike tsaye, lallai ne shugabanni masu kishi su motsa, su dauki kwararan matakan taka wa matsalolin nan birki.

Kuma hanya daya ce – MU TARU MU SAUYA HALAYENMU, MU TUNKARI GASKIYA DA GASKIYA!

Shin wai haka al’amura za su ci gaba da kasancewa?

A ce jiya kina cikin matsala, yau kina cikin matsala kuma gobe ma ki ce za ki kasance cikin matsala?

A yau Gizago (08065576011)