✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Najeriya ta kama hanyar rugujewa —Jega

Ma’aikata na da rawar da za su taka wajen gaggauta ceto Najeriya daga halin da take ciki.

Tsohon shugaban Hukumar Zabe ta Kasa mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega ya bayyana cewa, Najeriya ta kama hanyar rugujewa.

Farfesa Jega ya yi kira ga ’yan kasar da su tashi tsaye domin ceto kasar daga hannun wasu tsirarun mutane da ke tafiyar da al’amuranta ta karkashin kasa.

Jega, wanda Farfesa ne a fannin kimiyar siyasa a Jami’ar Bayero da ke Kano, ya ce, zaben 2023 na shugaban kasa zai kasance manuniya ga makomar Najeriya, kodai ta ci gaba da dunkulewa ko kuma ta wargaje, amma hakan ya ta’allaka ne da irin matakan da ma’aikata suka dauka.

Jega ya bayyana haka a wani taro da Kungiyar Kwadago ta NLC ta shirya a birnin tarayya Abuja, inda aka tattauna kan gudunmawar ma’aikata dangane da bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’umma.

Farfesan ya ce, ma’aikata na da rawar da za su taka wajen gaggauta ceto Najeriya daga halin da take ciki.

A bangare guda, shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya, Ayuba Wabba ya koka kan cewa, kasar ba ta taba shiga cikin wani mawuyacin hali ba tun lokacin da ta koma kan turbar demokuradiyya a shekarar 1999 kamar yanzu, yana mai cerwa, kasar ta zafafa gabanin zaben 2023 mai tafe.