✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya za ta dauki mataki a kan masu hana ’yan kasarta biza

Ministan ya ce daga yanzu Najeriyar za ta maida martani.

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa daga yanzu za ta mayar da martani a kan duk kasar da take kin bai wa ‘yan kasar takardar izinin shiga kasarta.

Bayanai sun ce dai ta kama hanyar cimma ruwa domin bayan kwashe shekaru ne ana muzgunawa ‘yan Najeriyar da ke neman takardun biza na shiga kasashen duniya ne gwamnatin Najeriyar ta dauki wannan mataki.

Ministan kula da harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo dai ya bayyana cewa lokaci ya wuce da Najeriyar za ta rinka bai wa ‘yan wasu kasashe izinin ziyarar kasar amma kuma a yi wa kasar kememe.

Ministan ya ce daga yanzu Najeriyar za ta maida martani.

Ana iya tuna cewa, tun a watan Oktobar bara ne Gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ta sake haramta wa ’yan Najeriya ziyartar kasarta ba tare da bayyana dalilinta na daukar wannan tsauttsauran mataki ba.

Kasar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta rarraba wa abokan huldar kasuwancinta daga Najeriya da suka hada da ejan-ejan da ke samar wa ’yan kasar takardun biza, matakin da ake ganin zai dada dagula rikicin diflomasiya tsakanin kasashen biyu.

Wannan na zuwa ne bayan ’yan makonni da Hadaddiyar Daular Larabawa ta tsaurara matakan bayar da biza ga sabbin bakin da ke marmarin shiga cikin kasar.

Sanarwar ta ce, hukumomin kasar sun soke daukacin bukatun neman takardun biza daga ’yan Najeriya da wasu kasashen Afirka na bakaken fata.