✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta kama mutum 7, ta lalata kadada 22 ta gonar Tabar Wiwi a Edo

NDLEA ta ce darajar gonakin Tabar ta kai miliyoyin Nairori.

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) reshen jihar Edo ta kama wasu mutum bakwai da take zargi, tare da lalata wasu gonakin Tabar Wiwi masu fadin kadada 22 a Jihar.

Hukumar dai ta ce darajar gonakin Tabar sun kai miliyoyin Nairori.

Da ya ke jawabi ga ’yan jarida jim kadan da kammala lalata gonakin, Mataimakin Kwamandan hukumar mai kula miyagun kwayoyi, Kenneth Obadike wanda shine ya jagoranci farmakin ya ce an cafke wadanda ake zargin ne a wata gonar Tabar da ke yankin Ughiedu a Karamar Hukumar Uhnwonde ta Jihar.

Ya ce wadanda ake zargin an dauko hayarsu ne a matsayin ’yan kwadago kuma gonar mallakin wani kasurgumin mai safarar miyagun kwayoyi ce.

”Mun shafe kusan kwana uku muna wannan aikin, mun kama mutum shida yayin farmakin farko, sai yau kuma muka kama bakwai lokacin da muke kokarin lalata gonar,” inji Mataimakin Kwamandan.

Kenneth ya kuma ce sun kama sinki 11 na Tabar Wiwin wacce aka riga aka sarrafa da nufin yin safararta daga gonar

“Mun gano gonakin Tabar Wiwi har guda uku, daya ta kai fadin kadada 4.47, ta biyun kuma ta kai kadada 15.47 sai ta ukun kuma mai fadin kadada 2.26.”

Ya kara da cewa sun gano gonakin ne da taimakon wasu bayanan sirri, inda ya ce suna ci gaba da fadada bincike don gano asalin wanda ya mallakesu.

Da yake hira da ’yan jarida, daya daga cikin wanda ake zargin ya ce an dauke shi ne a matsayin dan kwadago ya rika aiki a gonar bisa yarjejeniyar za a rika basi N120,000 duk shekara.

Wanda ake zargin wanda dan asalin Jihar Akwai Ibom ne ya ce a da yana aiki ne a wata gonar ayabar mutumin inda ake biyansa N75,000 duk shekara.

“Amma da ya yi min tayin aiki a gonar Tabar Wiwin bisa alkawarin N120,000, sai na amince saboda ina son in rage basussukan da ke kaina,” inji shi.