✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nigeria@62: Gwamnati ta ayyana Litinin a matsayin ranar hutu

A ranar Asabar ce Najeriya za ta cika shekara 62 da samun ’yancin kai

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, uku ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu albarkacin murnar cikar Najeriya shekara 62 da samun ‘yancin kai.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ne ya sanar da haka a madadin Gwamnatin Tarayyar a ranar Laraba.

Aregbesola ya yi amfani da dama wajen taya daukacin ‘yan Najeriya murnar zagayowar wannan rana.

Kana ya bai wa ‘yan kasa tabbacin gwamnati na ci gaba da yin bakin kokarinta don shawo kan kalubalen da suka dabaibaye Najeriya da kuma kyautata rayuwar ‘yan kasa.

Ranar daya ga watan Oktoba na kowace shekara, ita ce ranar da Najeriya ke gudanar da bukukuwan tunawa da samun ‘yancin kanta daga Turawan mulkin mallaka.