✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NLC ta soki ƙarin kuɗin lantarki

Ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta ƙi amincewa da shirin da ake yi na ƙara kuɗin wutar lantarki da kaso 40% nan da 1 ga Yulin…

Ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta ƙi amincewa da shirin da ake yi na ƙara kuɗin wutar lantarki da kaso 40% nan da 1 ga Yulin 2023.

A sanarwar da ya fitar a Abuja, Kwamared Ajaero ya ce shirin na nuna halin ko-in-kula da rayuwar talakawan Najeriya.

Hukumar kula da farashin lantarki ta ƙasa (NERC) ce ta amince da ƙarin kuɗin saboda tashin farashin man fetur da kuma karyewar darajar Naira.

Kanawa sun koka da rashin wutar lantarki

Ma’aikatan Lantarki za su shiga yajin aiki saboda cire tallafin man fetur

Sai dai shugaban na NLC ya buƙaci gwamnati ta hana wannan ƙarin kuɗin wutar.

A cewarsa “dole ne ayi la’akari da adadin wutar da kamfanonin rarraba wutar lantarki ke kawowa da kuma ƙarfin aljihun masu amfani da lantarki wurin biyan kuɗin”.