✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NSCDC ta kafa rundunar mata zalla don samar da tsaro a makarantu

Rundunar ta musamman za ta samar da tsaro a makarantu a fadin Najeriya.

Hukumar tsaro ta NSCDC ta kafa runduna ta musamman ta  mata zalla da za ta rika aikin samar da tsaro a makarantu a fadin Najeriya.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya ce hakan na daga cikin matakan da aka dauka karkashin shirin ‘Safe School Initiative’ domin samar da tsaro a makarantu.

Da yake bayani a yayen Rundunar a Katsina, Aregbesola ya yaba wa NSCDC bisa jagorancin da ta nuna wajen fara kafa rundunar mata zalla a matsayin wani bangare na kokarin shawo kan matsalar tsaro da ke addabar Najeriya.

Kakakin NSCDC, DCC Olusola Odumosu, ya ruwaito shi yana cewa baya ga inganta tsarin tsaro a makarantu, samar da rundumar zai kara wa aikin Hukumar nagarta.

Muhimmancin mata

Game da muhimmancin mata wajen yakar matsalolin tsaro, ministan ya ce kasancewar mata sun fiye da rabin ’yan Najeriya, ya dace a dama da su a duk ayyukan gina kasa.

Wasu daga cikin matan rundunar ta musamman a lokacin da suke atisaye. (Hoto:(Hoto: @raufaregbesola).

A cewarsa, bincike ya nuna duk abin da aka sanya mata a cikinsa ya fi samun karbuwa a wurin jama’a.

Ya ce matsalolin tsaro a Najeriya sun sanya hukumomi bullo da hanyoyi iri-iri na shawo kansu da kuma samar da aminci ga al’umma.

A don haka ya ba wa NSCDC tabbacin samun cikakkiyar goyon bayan Shugaba Buhari ta isassun kudade da biyan sauran bukatunta don gudanar da ayyukanta cikin nasara.

Garkuwa da dalibai

Babban Kwamandan Hukumar, Dokta Ahmed Audi, ya ce kafa rundunar ta mata zalla ya zama tilas, duba da karuwar matsalar garkuwa da dalibai da sauran ayyukan ’yan bindiga da sauransu.

A don haka, ya zama wajibi a dakile matsalar ta hanyar hana bata-garin kaiwa ga makarantu kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta ba da umarni.

Ya ce daga cikin matakan da NSCDC ta dauka, har da tabbatar da ingataccen tsaro a makarantun da yanayin tsaronsu ke da rauni.

“An yi hakan ne domin tabbatar da tsaron dalibai da kuma bayar da kwarin gwiwa garesu da iyayensu da malamai da ma daukacin al’umma,” kamar yadda ya bayyana.

Dakarun rundunar ta musamman na nuna bajintarsu a wurin bikin yayensu. (Hoto: @raufaregbesola).

Ya ce hukumar ta kammala tattara bayanan yanayin tsaro a makarantu domin yin gyare-gyare a wuraren da suka dace da kuma bullo da hanyoyin tabbatar da nasara wajen ba su cikakkiyar kariya.

Nuna kwarewa

Babban Kwamandan na NSCDC ya yaba wa dakarun rundunar bisa hazakar da suka nuna a lokacin kwas din da aka yi musu, ya kuma bukace su da su nuna kishi da kwarewa yayin gudanar da ayyukansu.

Ya ja hankalinsu da su yi dabbaka darussan da suka koya, sannan su guji duk abin da zai iya zubar da kimar Hukumar.