✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP na da yakinin samun nasara a zaben 2023 —Secondus

Secondus ya bukaci Matawale ya tuna yadda aka yi ya zamo Gwamnan Zamfara.

Jam’iyyar adawa a Najeriya ta PDP, ta ce tana da yakinin samun nasara a babban zaben kasa na 2023 duk da cewar wasu daga cikin gwamnoninta sun sauya sheka zuwa APC.

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Mista Uche Secondus ne ya bayyana hakan a Abuja yayin da yake martani kan sauya shekar da Gwamnan Jihar Zamfara, Mohammed Bello Matawalle ya yi zuwa APC.

  1. Yadda kwacen waya ke zama ajalin jama’a a Najeriya
  2. Kotu sa a kashe dan fashi ta hanyar yatayewa

“APC tana bibiyar gwamnoninmu, muka mun maida hankalinmu ga talakawan kasar nan.

“Gwamnonin suna da kuri’a daya ne, mu kuma muna tare da ’yan kasa da talakawa.

“Talakawa suna tare damu kuma suna son PDP don haka ina bada tabbacin zamu kafa gwamnati a 2023, saboda talakawa ba don gwamnoni ba,” a cewar Secondus.

A cewar Secondus, yawancin gwamnonin sun bar PDP ne saboda tsoron tursasawa.

Ya ce jam’iyyar na farin ciki cewa mafi yawan talakawan jihohinsu musamman a Zamfara ba su bar su ba.

Yadda Matawalle ya zamo gwamnan jihar Zamfara

Secondus ya ci gaba da cewa, “Ga dukkan alama Matawalle ya manta yadda aka yi ya zama Gwamnan Zamfara.

“Matawalle na bukatar a tunatar da shi cewa babu wata doka da ta ba shi damar tsallakawa zuwa wata jam’iyya, baya ga dokar da ta ba PDP hurumi a akwatin zabe”.

Secondus, ya kara da cewar hukuncin kotun koli ne ya ba shi damar zama Gwamnan Zamfara, kamar yadda Kundin Tsarin Mulki na 1999 ya tanadar.

“Jami’iyyar siyasa ce kadai ke da damar tsayawa takara ba mutum ba, don haka idan aka samu nasara jam’iyya ce take da wannan nasara ba wanda aka zaba ba.

Secondus ya gargadi ’yan majalisar Jihar Zamfara a kan kada su bari a tursasa su wajen rasa kujerunsu ta hanyar sauya sheka zuwa APC.

“Babu wata rarrabuwar kai da aka samu a cikin PDP da za ta sanya wani sauya sheka daga wani dan majalisarmu.

“PDP na fatan cewa Matawalle da ’yan majalisar Tarayya da na Jiha daga Zamfara da suka sauya sheka za su yi taka tsantsan kan hukuncin da zai biyo baya,” in ji shi.

Kazalika, ya jaddada da rusa Kwamitin Zartarwa na Jam’iyyar a jihar, wanda kundin tsarin mulkin PDP na 2017 ya tanada a karkashin sashe na 29 sakin layi na biyu.