✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

PDP ta jajanta wa APC kan hatsarin jirgin ruwan magoya bayanta a Delta

Hatsarin ya auku ne a lokacin yakin neman zaben dan takarar gwamnan APC a jihar.

Jam’iyyar PDP a Jihar Delta ta jajanta wa APC kan hatsarin jirgin ruwa da magoya bayanta suka yi a yankin Okerenkoko, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Sakataren Yada Labaran PDP a jihar, Ifeanyi Osuoza ne, ya bayyana hakan cikin wani sakon ta’aziyya da ya aike wa APC a garin Asaba.

“PDP a Delta ta kadu da samun labarin hatsarin jirgin ruwa a yankin Okerenkoko na Karawar Hukumar Warri ta Kudu maso Yamma, wanda ya yi ajalin magoya bayan APC.

“Hatsarin da ya yi ajalin mutum biyu, yayin da wasu suka ji rauni wasu kuma suka bace, abun a tausaya ne.

“Muna jajanta wa mataimakin shugaban majalisar dattawa kuma dan takarar gwamnan APC, Sanata Ovie Omo-Agege da dukkanin iyalan APC.

“Muna fatan samun rahama ga wadanda suka mutu, wadanda suka ji rauni muna musu fatan murmurewa cikin kankanin lokaci,” in ji sanarwar.

Aminiya ta ruwaito yadda mutane biyu suka mutu, uku kuma sun bace a yayin dawowa daga yakin neman zaben Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kuma dan takarar Gwamnan Jihar Delta a Jam’iyyar APC, Sanata Ovie Omo-Agege.