✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP za ta kalubalanci tsige Mataimakin Gwamnan Zamfara a kotu

PDP ta ce tsigewar ba ta kan ka’ida kuma haramtacciya ce.

Jam’iyyar PDP ta ce tana nan tana shirye-shiryen garzayawa kotu don ta kalubalanci tsige Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Mahdi Aliyu, da Majalisar Dokokin Jihar ta yi.

PDP ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da Sakataren Yada Labaranta na kasa, Mista Debo Ologunagba, ya fitar a Abuja.

Sanarwar ta ce tsigewar ba ta kan ka’ida kuma haramtacciya ce.

“PDP na nazari a kan karan tsayen da aka yi wa doka a jihar Zamfara, don daukar matakin da ya dace.

“Saboda haka, PDP da mutanen Zamfara ba za su lamunci wannan karan tsayen ba, kuma suna nan suna duba yiwuwar garzayawa kotu don kwato hakkinmu.

“Jam’iyyarmu na da kwarin gwiwar cewa bangaren shari’a, wanda a lokuta daban-daban a baya ya nuna cewa yana tabbatar da bin doka da oda, zai yi adalci” inji sanarwar.

A ranar 22 ga watan Fabrairu ne Majalisar Dokokin Jihar ta tsige Mahdi Aliyun daga mukaminsa.

Matakin ya biyo bayan kudurin da Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Faruku Dosara (APC, Maradun 1) ya gabatar a zauren majalisar.

Gwamnan Jihar ta Zamfara, Bello Matawalle dai ya zama Gwamnan Jihar ne a karkashin jam’iyyar PDP, kafin daga bisani ya sauya sheka zuwa APC a ranar 28 ga watan Yunin 2021.

Sai dai dangantaka ta yi tsami ne tsakanin Gwamman da Mataimakinsa lokacin da Mahdin ya ki bin Matawallen zuwa APC. (NAN)