✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

PSG ta dauki Pochettino a matsayin sabon kocinta

Kafin zama sabon mai horar da kungiyar ta PSG, ya horar da kungiyar Espanyol, Southampton da kuma Tottenham.

Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta dauko Mauricio Pochettino a matsayin sabon mai horas da ’yan wasanta.

PSG ta nada Pochettino ne bayan sallamar Thomas Tuchel da ta yi a satin da ya gabata.

Tuchel ya shekara biyu da rabi yana jan ragamar kungiyar ta PSG.

Kafin sallamarsa ya lashe gasar cin kofin Ligue 1 na kasar Faransa har sau biyu, sai gasar Coupe de France and Coupe de la Ligue.

Kafin zaman Pochettino sabon kocin kungiyar, ya horar da kungiyar Tottenham, kafin a sallame shi a watan Nuwamban 2019.

Pochettino, ya horar da kungiyar Espanyol daga 2009 zuwa 2012, daga nan ya karbi ragamar Southampton sannan Tottenham.

Kafin zamansa mai horarwa, ya buga wasa a matsayin dan wasan PSG a shekara ta 2001 zuwa 2003.