✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rikici ya sa mutum 9,000 hijira a Sudan ta Kudu —MDD

Ba a tantance adadin mutanen da suka mutu da wadanda aka yi wa fyade a rikicin baya-bayan da ya barke a Kudancin Sudan ba.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa sama da mutum 9,000 rikici ya daidaita a baya-bayan nan a yankin Kudancin Sudan.

Majalisar ta ce a halin da ake ciki, sansanin ’yan gudun hijira da ke Malakal ya batse da sabbin ’yan gudun hijira daga Kudancin Sudan.

Bayanai sun nuna hare-hare sun tilasta wasu mazauna yankin buya a cikin fadamu da dazuzzuka don tsira da ransu.

A cewar Majalisar, ba a kai ga tantance adadin wadanda suka mutu da wadanda aka yi wa fyade ba saboda kazancewar rikicin yankin.

Kazalika, an samu rahotanni da dama dangane da sace mutane da yawan gaske a yankin, in ji MDD.

Rahotanni sun ce, kaso 75 cikin 100 na sabbin ’yan gudun hijirar, mata ne da kananan yara.