Rikicin APC a Kano ba zai dauke min hankali ba —Ganduje | Aminiya

Rikicin APC a Kano ba zai dauke min hankali ba —Ganduje

Abdullahi Ganduje, Gwamnan Jihar Kano
Abdullahi Ganduje, Gwamnan Jihar Kano
    Ishaq Isma’il Musa da Zahraddeen Yakubu Shuaibu, Kano

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya ce rikicin jam’iyyar APC da ya yi kamari a jihar ba zai dauke masa hankali ba daga ci gaban jihar da ya sa a gaba.

Ganduje, a cewar Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnatin Kano, Abba Anwar, ya bayyana hakan ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar ranar Lahadi a Fadar Gwamnatin Kano.

A cewarsa, “Yana da matukar muhimmanci kowa ya fahimci cewa hazakarmu da gogewarmu a siyasa ba za su bari wani dan karamin rikicin jam’iyya ya karkatar da hankalinmu wajen raya jiharmu ta Kano ba.

“Abin da ke faruwa a halin yanzu ba wani abu ba ne face wani bangare na siyasa da ya zama al’ada a tsarin dimokuradiyya.”

Ganduje ya ce an gudanar da wannan taro ne domin jaddada bukatar zaman lafiya a jam’iyyar.

Ya ce, “Bai kamata hankalinmu ya karkata ba saboda wani dan karamin rikicin siyasa na jam’iyya da ba kanshi farau ba.

“Wannan abu ne na al’ada a tsarin mulkin dimokuradiyya,” a cewar Ganduje.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Sanata Kabiru Gaya, mambobin Majalisar Wakilai ta Tarayya na jihar, Shugaba da mambobin Majalisar Dokokin jihar, shugabannin kananan hukumomi, shugabannin Jam’iyyar APC da sauransu.