✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin manoma da makiyaya ya sake yin ajalin mutum 9 a Jigawa

Rikicin na zuwa ne kasa da mako biyu bayan makamancinsa ya hallaka mutum 6 a Jihar

Akalla mutum tara ne suka rasa ransu, wasu da dama kuma suka jikkata a sabon rikicin da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a Karamar Hukumar Guri ta Jihar Jigawa.

Sabon rikicin dai na zuwa kasa da mako biyu bayan makamancinsa ya yi ajalin mutum shida a Karamar Hukumar Gwaram ta Jihar, ko da dai ’yan sanda sun ce mutum biyu ne.

Rahotanni daga yankin na cewa sakamakon rikicin, harkokin kasuwanci sun tsaya cik, saboda manoma da makiyaya ba sa iya kai amfanin gona da dabbobinsu kasuwa.

Kazalika, lamarin ya yi sanadiyyar rufe makarantar Firamare ta makiyaya da ke yankin, saboda kauce wa harin ramuwar gayya.

Garuruwan da rikicin ya fi shafa dai sun hada da Gagiya da Dawa Guri da kuma Megrami.

Jami’in yada labarai na Karamar Hukumar, Sani Doro, ya ce akalla manoma hudu ne aka kashe da kuma makiyaya biyar.

Ya ce kodayake akwai alamun lafawar kura a yankin, har yanzu mutane na tsoron fitowa daga gidajensu saboda fargabar hari.

Shi ma wani Kwamandan Hisbah a yankin, Umar Yuguda, ya ce dabbobin makiyaya sun lalata gonakin shinkafa da na alkama da na masara da dama.

Ya ce ba a taba samun irin wannan rikicin ba a tarihin garin, kodayake ya ce jami’an tsaro na aiki tukuru wajen dawo da zaman lafiya.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar, ASP Lawan Shisu Adam, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma ce an kama mutum 10 da ake zargi da hannu a ciki.

Sai dai ya ce mutum daya ne ya rasa ransa, yayin da bakwai kuma suka jikkata kuma yanzu suna Babban Asibitin garin Hadejia, inda suke samun kulawa.