✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin sarauta: An sanya dokar hana fita a Ondo

An shafe kwanaki ana kazamin rikici kan sarautar Oloja a yankin Ikare.

An sanya dokar hana fita ta sa’a 24 bayan barkewar rikici kan sarauta a Jihar Ondo.

Dokar hana fitar da ta fara aiki karfe 6 na yammacin Laraba a yankin Ikare ta biyo bayan kwanakin da aka yi ana kazamin rikici a garin Ikare-Akoko da ke Karamar Hukumar Akoko ta Arewa-maso-Gabas ta jihar.

“Duk wanda aka samu yana karya dokar zai yaba wa aya zaki,” inji sanarwar Gwamnatin Jihar wadda ta kuma girke jami’an tsaro a yankin.

Rikicin ya samo asali ne bayan takaddama ta barke kan kujerar sarautar Olokoja, har ta kai ga kone-konen motoci a kan titunan garin.

Shaidu sun ce an yi ta harbe-harbe, a yayin da bangarorin da ke rikcin suka fito da makamai suna gwabza fada a tsakaninsu.

Hakan ta sa wasu mazauna yin kaura, kafin a girke sojoji da ’yan sanda, amma duk da haka kurar ba ta lafa ba.

“Nan take gwamnati ta dakatar da duk abubuwan da suka danganci sarautar Oloja, ta kuma haramta kowa gabatar da kansa a matsayin mai rike da ita ko goyon bayanta ta kowace fuska”, inji sanarwar da Kwamishinan Yada Labaran Jihar, Donald Ojogo ya sanya wa hannu.