✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ruwan sama ya yi ajalin mutum 11 a Rwanda

Ruwan saman ya ci gidaje 100 da gonaki masu fadin hekta 50 baya ga sauran asarar da aka tafka.

Akalla mutum 11 ne aka tabbatar da mutuwarsu, bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya a sassan kasar a kasar Rwandaa ranar Asabar, a cewar ma’aikatar bayar da agajin gaggawa ta kasar.

Ma’aikatar ta ce bakwai daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su sun rasu ne gundumar Nyamasheke da ke Yammacin kasar, uku kuma a Kigali babban birnin kasar.

Ma’aikatar ta ce wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, sun mutu ne sakamakon zaftarewar kasa, wasu kuma suka mutu bayan ruftawar gidajensu..

An samu zaftarewar kasar da ta yi sanadin rushewar gidan wani mutum ta kashe ’ya’yansa uku tare da raunata daya a gundumar Nyamasheke.

Ma’aikatar ta ce wasu mutane 13 a gundumomi daban-daban sun jikkata sakamakon mamakon ruwan saman, wanda kuma ya yi sanadiyyar rushewar gidaje 100 a yankuna daban-daban na kasar.

Kazalika abubuwa da dama da suka hadar da igiyoyin wutar lantarki, gadoji da kuma gonaki kusan hekta 50 da ke Gabashin kasar, sun salwanta.

Ana dai ci gaba da shirye-shiryen tallafa wa mutanen da abin ya shafa don sama musu matsuguni.

Ana sa ran kasar Rwanda za ta samu ruwan sama mai karfi daga ranar 21 zuwa 30 ga watan Afrilu, kamar yadda hukumar hasashen yanayi ta kasar ta bayyana.