✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ruwan sama ya yi ajalin mutum biyar a Damaturu

Kimanin mutum 41 ne lamarin ya rutsa da su a Damaturu.

Kimanin mutum biyar ne suka rasa rayukansu yayin da gommai suka jikkata bayan saukar wani mamakon ruwan sama mai tafe da kakkarfar iska da guguwa a Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta jihar SEMA ta tabbatar da afkuwar lamarin inda ta ce fiye da gidaje 100 ne suka lalace sakamakon iftila’in.

Sakataren SEMA na jihar, Mohammed Goje ya ce sun samu labarin lamarin ne daga wasu mutane a ranar Litinin 9 ga watan Mayun 2022, wadanda suka taimaka wajen gaggawar kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

Mohammed Goje ya kuma tabbatar da cewa mutum biyar sun riga mu gidan gaskiya daga cikin 41 da lamarin ya rutsa da su, kuma mutanen sun fito ne daga yankuna daban-daban a birnin na Damaturu, inda aka wuce da su asibiti.

Yankunan da abin ya shafa sun hada da Waziri Ibrahim Extension da Abbari Extension da NayiNawa da Pompomari da rukunin gidajen ‘yan Majalisar Dokokin jiha da Gujba Road da kuma Maisandari.