✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabon albashi: Za a koma biyan N30,000 a Gombe

Daga Janairun 2021za a ci gaba da biyan sabon albashin da aka dakatar a baya

Gwamnatin Jihar Gombe ta ce za ta ci gaba da biyan ma’aikatanta mafi ƙarancin albashi na N30,000 daga watan Janairun 2021.

Kwamishinan Kudi da Bunkasa Tattalin Arziki na Jihar Gombe, Muhammad Gambo Magaji, shi ne ya bayyana haka a lokacin da yake bayanin kasafin kudin Jihar na 2021.

Ya ce watan Maris na bara Gwamantin Jihar ta dakar da biyan sabon mafi karancin albashi na N30,000 ne saboda karancin kudaden shiga da ta yi fama da shi.

 Magaji ya ce a wancan lokacin an dakatar da biyan sabon albashin ne bayan an fara biyan shi da wata daya a Jihar.

Kwamishinan ya ce amma a kasafin bana, Gwamantin Jihar ta shirya ci gaba da biyan sabon albashin, wanda ya ce shi ya sa kason da aka ware wa kudaden ma’aikata  a kasafin ya karu.

Ya ce kasafin jihar da aka rattaba wa hannu ya kuma rage kudaden gudanar da gwamnati zuwa kasa da kashi 10% na kasafin, da zummar inganta rayuwar al’ummar Gombe.

A cewarsa, hakan “sabanin yadda gwamnatocin baya suke ware kashi 25% na kasafin kudin jihar domin gudanar da gwamnati.”