✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sarkin Musulmi ya ziyarci Wike a Fatakwal

Sarkin da Gwamna Wike sun yi wata ganawa a bayan labule.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya gana da Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike a Fatakwal.

Wakilinmu ya rawaito cewa, Sarkin ya gana da gwamnan ne a wata ziyarar ban girma da ya kai Fadar Gwamnatin Jihar a ranar Juma’a.

Ganawar tasu na zuwa ne a daidai lokacin da Sarkin Musulmin ya ziyarci babban birnin jihar domin bude taro Hadaddiyar Kungiyar Mata Musulmai ta kasa da aka yi a jihar.  

Bayanai sun ce Sarkin Musulmin yana sauka a garin kai tsaye ya zarce gidan gwamnatin jihar inda suka shiga wata ganawa ta sirri.

Gwamna Wike tare da Mai Alfarma Sarkin Musulmi da shugabannin kungiyar mata ta kasa