✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Zazzau ya nada sabon Iyan Zazzau

Sarki Ahmad Bamalli ya daga martabar wanda ya yi takarar neman sarauta da shi

Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli ya nada Dan Majalisar Tarayya Mai wakilatar Mazabar Zariya, Abbas Tajuddeen a matsayin sabon Iyan Zazzau, bayan rasuwar Alhaji Bashar Aminu.

Sarkin Zazzau ya kuma daga matsayin daya daga cikin ’ya’yan sarki da suka yi takarar kujerar Sarkin Zazzau da shi kuma Yeriman Zazzau, Alhaji Munir Jafar zuwa Madakin Zazzau.

Da yake tabbatar wa Aminiya da sabbin nade-naden, akawun Masarautar Zazzau, Alhaji Abubakar Ladan ya bayyana cewa sarautar Madakin Zazzau ita ce ta biyu mafi martaba a Masaratutar.

Alhaji Abubakar Ladan ya kara da cewa Sarkin ya nada dan marigayi Iyan Zazzau Bashar Aminu, wato Alhaji Abdulkarim Bashir Aminu, a matsayin sabon Talban Zazzau, sarautar da Alhaji Abdulkadir Iya-Pate ke rike da ita kafin ya rasu.

A ranar Juma’a 1 ga watan Janairu, 2021 Fadar Sarkin Zazzau ta sanar da rasuwar Iyan Zazzau Alhaji Bashar Aminu da kuma Talban Zazzau Alhaji Abdulakadir Pate.

Sauran sabbin nade-naden da aka yi a sun hada da na sabon Dan Iyan Zazzau wanda aka ba wa Mai Shari’a Munir Ladan.

Sarautar Magajin Garin Zazzau, wadda Sarki Ahmed Bamalli ke rike da ita kafin zamansa Sarkin Zazzau kuma an bayar da ita ga kaninsa, Alhaji Mansur Nuhu Bamalli.

Kafin sarautarsa ta yanzu, Alhaji Munin Nuhu Bamalli shi ne ke rike da sarautar Barde Kerarriya wadda yanzu aka ba wa Alhaji Buhari Aminu Ciroma.

Kazalika na ba da sarautar Barden Zazzau ga Alhaji Shehu Tijjani, yayin da ta Sa’in Zazzau  kuma aka bayar da ita ga Alhaji Idris Ibrahim Idris.

Aminu Iya Sa’idu kuma shi ne sabon Kogunan Zazzau, sabon Barden Kudu kuma shi ne Alhaji Bashar Abubakar.

Alhaji Abubakar Ladan ya ce kowanne daga wadanda aka ba wa sabbin sarautun ya riga ya karbi takardar shaidar nadin sa.

Nade-naden na zuwa ne kasa da mako biyu da rasuwar Iyan Zazzau Alhaji Bashar Aminu, wanda Allah Ya yi wa cikawa sakamakon rashin lafiya.