✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Saudiyya ta ba mata 32 lasisin tuka jirgin kasa na Masallacin Harami

Matan za su rika tuka maniyyata ne a Masallacin Harami

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Kasa ta Saudiyya (SAR) ta ba wasu mata su 32 lasisin tuka jirgin kasan da yake sufurin maniyyata a Masallacin Harami da ke birnin Makkah.

Sun fara tuka jirgin ne bayan wasu kwararru 12 a Kwalejin Fasahar Tukin Jirgin Kasa ta kasar sun horar da su na tsawon wata 12.

Kamfanin Dillancin Labaran Saudiyya (SPA) ya rawaito cewa mata da dama a kasar ne suka nuna sha’awarsu ta aikin tuka jiragen.

Daya daga cikin direbobin, Tharaa Ali Alzahrani, ta ce, “Lokacin da Kwalejin Tukin Jiragen Kasa ta Saudiyya ta sanar gurbin ayyukan a watan Janairu, na nuna sha’awar neman aikin, inda bayan an tantance mu, aka dauke mu.

“Hakan ya sa na yi matukar alfahari saboda na sami damar hidimta wa kasata. An koya mana tuki a karance da kuma a aikace,” in ji ta.

Ita kuwa Rotella Yasser Najjar cewa ta yaba wa mahukuntan kasar saboda ba matan damar yin aiki a bangarori daban-daban, ciki har da a Masallacin na Harami.