✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta wajabta wa alhazai karbar rigakafin COVID-19

Ba za ta ba da biza ga alhazai ba, sai dole an yi musu rigakafin cutar

Kasar Saudiyya ta wajabta karbar allurar rigakafin cutar COVID-19 a matsayin sharin amince wa maniyyata aikin Hajji sauke farali.

Yayin ba da umarnin, Ministan Lafiya na Saudiyya Tawfiq Al-Rabiah ya ce ya zama tilas ga maniyyata yi karbi rigakafin na COVID-19, domin  kasar ba za ta ba da izinin shigar kasar don aikin Hajji ba, sai dole idan an yi masa rigakafin.

Rabiah ya ce: “Dole ne ku shirya da wuri don tabbatar da karfin da ake bukata don gudanar da cibiyoyin kiwon lafiya a Makkah da wurare masu masu tsarki da Madina, da kuma wuraren da mahajjata za su shiga lokacin aikin Hajjin na 2021.”

Ya kara da cewa: “Dole ne a kafa Kwamitin Yin Allurar Rigakafin kwarkwata ga mahajjata da masu Umrah.

“Dole ne a yi rigakafin COVID-19 ga masu son shigowa domin aiki saboda hakan na daga cikin sharuddan aikin Hajjin mai zuwa,” a cewarsa.