✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta yi gargadi kan ruwan ZamZam na jabu a wasu sassan duniya

An samu gurbattacen ruwan ZamZam a Birtaniya da Afirka da kuma Australia.

Hukumomin Saudiyya sun gargadi al’ummar musulmi kan yaduwar ruwan ZamZam na jabu a wasu sassa na duniya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin kasar ke kokarin daukar matakan magance yaduwar ruwan ZamZam na jabu da aka gani a wasu kasashen duniya.

Shafin Haramain da ke dandalin Twitter na hukumomin da ke kula da Masallatai Biyu Masu Daraja na Saudiyya sun wallafa hotunan robobin ruwan ZamZam na gaskiya domin ankarar da al’umma.

“Sakamakon rahotannin da ake samu na gurbataccen ruwan ZamZam a sassa daban-daban na duniya da suka hada da Birtaniya da Afirka da kuma Australia.

“Wadannan su ne hotunan robobin ruwan ZamZam na gaskiya ba na jabu ba,” a cewar sanarwar.