✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Saura kiris a saki sabuwar kira’ar Sudais

“Na gaba kadan za a sakki abon karatun Sheikh Sudais ta talabijin, rediyo da kuma intanet.”

An kammala daukar karatun Babban Limamin Masallacin Harami, Sheikh Abdulrahman Sudais a ‘studio’ kuma ana dab da sakin sa a fadin duniya.

Rahotanni sun ce karon farko ke nan a tarihi da fitaccen malamin — wanda miliyoyin Musulmi a fadin duniya ke kwaikwaon kira’arsa — ya amince ya gudanar da karatu a nadi kira’arsa a daukin daukar shirye-shirye.

Hukumar Masallacin Harami ta sanar a ranar Alhamis cewa, “Dakin gabatar da shirye-shire na Masallacin Harami ya kammala daukar kira’ar Sheikh Abdul Rahman Sudais.

“Na gaba kadan za a yada karatun nasa ta talabijin, rediyo da kuma intanet.”

Sheikh Sudai dai shi ne Shugaban Majalisar Kula da Masallatan Harami na Kasar Saudiyya, kuma ya shafe shekaru da dama yana limancin Juma’a, Sallar Tahajjud da sauransu.