✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shawarwarin shugabannin Afirka domin sasanta rikicin Rasha da Ukraine

Tawagar karkashin jagorancin Cyril Ramaphosa ta gabatar wa Rasha da Ukraine da shawarwari har guda 10.

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya bayyana ziyarar da shugabannin Afirka suka kai cikin makon da ya gabata a kasashen Ukraine da Rasha a matsayin wadda ke cike da tarihi, duk da cewa babu wani takamaimen sakamako da wannan ziyara ta samar.

A wani sako da ofishinsa ya fitar a wannan Litinin, shugaba Ramaphosa ya bayyana ziyarar a matsayin wadda tarihi ba zai taba mantawa da ita ba, sannan hakan na kara tabbatar da cewa Afirka za ta iya taka gagarumar rawa, ba wai a nahiyar kawai ba.

Ita dai wannan tawaga ta shugabannin Afirka karkashin jagorancin Cyril Ramaphosa, ta gabatar wa kasashen Rasha da Ukraine da shawarwari har guda 10, wadanda matukar aka aiwatar da su, za a samu zaman lafiya.

Daga ciki har da gaggauta tsagaita wuta, da mutunta ’yancin kowace kasa, bayar da damar yin amfani da tashoshin jiragen ruwan kasashen biyu domin fitar da abinci zuwa sassan duniya da kuma yin musayar fursunonin yaki.

Ramaphosa ya ce, daya daga cikin nasarorin da wannan ziyara ta samu ita ce amincewar da shugabannin kasashen biyu suka yi domin ganawa da takwarorinsu na Afirka.

Wannan dai tawaga ce da ta kunshi shugaban Afirka ta Kudu, na Senegal, Comoros da kuma Zambia, sai kuma manyan jami’i na gwamnatocin kasashen Uganda, Masar da kuma Congo Brazzaville.

An tambayi Kingsley Makhubel, tsohon jami’in diflomasiyya kuma mai sharhi kan al’amuran rikice-rikice a Afirka ta kudu, “Shin mece ce hikimar wannan yunƙuri na masu shiga tsakanin?”

Sai ya ce ayarin wani batu ne da ba a saba ganin irinsa ba, inda aka samu ayarin shugabannin Afirka mafi girma da suka tunkari batun kashe wutar yakin da wasu ke ganin tamkar yin fito-na-fito ne tsakanin Rasha da Kasashen Yamma.

Sannan wani gagarumin yunkurin shiga tsakani na diflomasiyya ne zuwa wajen nahiyar, “batu ne da za a yi maraba da shi.”

Kuma zai kara bai wa Afirka damar yin magana da babbar murya a zauren Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kasashen duniya, kamar yadda daraktan cibiyar kwararrun masana harkokin rikici ta duniya ICG reshen Afirka, Murithi Mutiga, ya bayyana.

Jean-Yves Ollivier, shugaban gidauniyar Brazzaville Foundation, da ke kokarin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban Afirka mai babban ofis a Birtaniya, ya ce mnufar ziyarar ita ce fara tattaunawa maimakon warware rikici.

A fara tattauna batutuwa kai tsaye wadanda ba su shafi yanayin ayyukan soja ba, da kuma fara ginawa daga inda aka tsaya.

Daya daga cikin batutuwan shi ne yiwuwar musayar fursunonin yaki a tsakanin Rasha da Yukren.

Batu na gaba shi ne yadda za a yi kokarin warware batutuwan da suka fi shafar Afirka, kamar samar da hatsi da takin zamani.

Yakin ya yi matukar illa wajen hana fitar da hatsi daga Yukren da kuma takin zamani daga Rasha, lamarin da ya haifar mummunan karancin abinci a duniya.

Afirka, wadda ta dogara kacokam wajen shigo da duk kayayyakin, tana matuƙar ɗanɗana kuɗar da ba ta taba ba.

Mista Ollivier ya ce, shugabannin na Afirka za su yi kokarin shawo kan Rasha a kan ta amince ta tsawaita yarjejeniyar nan da aka yi watsi da ita, ta bai wa jiragen ruwan Yukren damar fitar da hatsi ta tekun Baharul-Aswad.

Sannan za su bukaci hukumomin Kyiv su taimaka wajen lalubo hanyoyin sassauta matakan hana fitar da takin zamani na Rasha wanda a halin yanzu aka jibge a tashoshin ruwa.