✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shekara 12 da rasuwar Umaru Musa Yar’Adua

Ya rasu bayan shekara uku a kan mulki ranar 5 ga watan Mayu, 2010.

A ranar 5 ga watan Mayu 2022 tsohon Shugaban Kasar Najeriya, Umaru Musa Yar’Adua ke cika shekara 12 da rasuwa.

Marigayi Umaru Musa Yar’Adua,  ya rasu ne a shekarar 2010 sakamakon rashin lafiya, shekara uku bayan zamansa shugaban kasa a shekarar 2007.

Gwamnatin Umaru Musa Yar’Adua ta yi fice da Manufofi Bakwai da ta gabatar, da kuma yadda shi kansa ya amince da cewa zaben 2007 mai cike da rudani da ya kawo shi kan kujera na cike da kura-kurai, ya kuma daura damarar gyarawa.

Bangarorin da gwamnatinsa ta ba wa fifiko su ne na wutar lantarki, makamashi da ababen more rayuwa; wadata kasa da abinci; samar da arziki; sufuri; tsaro; ilimi; samar da ayyuka; sai kuma gyara dokokin kasa da filaye.

Marigayin wanda aka haifa a ranar 6 ga watan Agusta, 1951, ya kasance Gwamnan Jihar Katsina daga 1999 zuwa 2003, inda ya gudanar a muhimman ayyuka da ake ganin har yanzu gwamnatocin da suka biyo baya ba su kama kafarsa ba.

A lokacin da yake gwamanan Katsina, ya kasance gwamnan farko da ya bayyana kadarorinsa a bainar jama’a sannan ya kawo muhimman ayyukan ci gaba.

Shi ne gwamna na biyar a Arewacin Najeriya da ya fara dabbaka shari’ar Musulunci, ya gina makarantu, kuma ana ganin ya cika alkawarinsa na gudanar da gwamnati cikin gaskiya da rashin almundahana.

Bayan rasuwarsa ne mataimakinsa, Goodluck Jonathan ya zama shugaban kasa, ya karashe wa’adinsa zuwa shekarar 2011, daga bisani ya yi nasa wa’adin daya zuwa 2015, inda aka kayar da shi a lokacin da yake neman tazarce.

Da yake jawabi kan tsohon uban gidan nasa, Jonathan ya bayyana marigayi Umaru Musa Yar’ Adua, a matsayin jagora mara son zuciya, wanda “samun irinsa sai an tona” a Najeriya.

Jonathan ya ce, “Shekara 12 da suka gabata kasarmu ta rasa dan kishin kasa, mara son zuciya, mai son zaman lafiya wanda ya yi shugabanci da gaskiya da kishin al’umma.

“A yanzu Marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua ba ya tare da mu, amma ba za mu taba mantawa da shi ba saboda ayyukan da ya yi da suka shafi rayuwa za su ci gaba da tunatar da mu game da shi.

“Ya kasance soja mai kare gaskiya da adalci da manufofin dimokuradiyya, ya hidimta wa al’umma; da wuya a samu irinsa.

“Ubangidana ne.

“Shugaba Yar’Adua, a yau muna tunawa da kai kuma za mu ci gaba da tunawa da kyawawan ayyukan da ka yi wa kasar nan.

“Ka kasance shugaba mai kishin kasa kuma ka hidinma wa al’umma.”