✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin da gaske Dogo Gide ya mutu?

Ana rade-radin ya mutu ne a wani asibiti a Sakkwato inda yake jinyar rauni da ya samu sanadiyyar harbin bindiga.

Tun jiya Laraba ne aka fara yada hoton wani mamaci, inda ake cewa gawar fitaccen kasurgumin dan ta’addan nan Dogo Gide ne.

Rahotanni sun bayyana cewa ya mutu ne a wani asibiti a Sakkwato bayan jinyar da ya yi sakamakon a harbinsa da bindiga da aka yi

Asibitin da aka ce ya yi jinya

Hukomomin Asibitin Relience Specialist Hospital da Sakkwato ya ƙaryata batun cewa Dogo Gide ya kwanta jinya a wajensu, ballanta ma ya mutu.

A wata sanarwa da suka fitar, sun ce, “Mun samu labarin da ake yadawa cewa wani jagoran ’yan bindiga Dogo Gide ya kwanta a asibitinmu har ya mutu.

“Wannan labarin ba gaskiya ba ne. Ko kaɗan babu wani mai laifi da ya kwanta a asibitinmu, ballanta ma a ce fitaccen ɗan bindiga haka. Muna kira da a yi watsi da wannan labarin.”

Wata majiya a yankin Dansadau ta bayyana wa Aminiya cewa da a ce da gaske Dogo Gide ya mutu, da yanzu labarin ya karade ko’ina.

A cewar majiyar, “Har yanzu babu tabbaci ko kuma wata alama da muka gani a nan yankin Dansadau.

“Wadanda suke cewa ya mutu sun ce wai daga Shiroro aka ɗauko shi zuwa Sakkwato domin jinya. Wannan zai yi matuƙar wahala,” inji majiyar.

Sa hannu a sakin ɗaliban Kuriga

Wata majiyar ta kara da cewa, lallai Dogo Gide ya samu rauni a farmaki da sojoji suka kai masa, amma tana shakkun mutuwarsa kasancewa ya taimaka wajen sako ɗaliban makarantar Kuriga a ranar Lahadin da ta gabata.

“Wanda ya kitsa sace daliban mai suna Yellow Janbros yaron Dogo Gide na a da kafin suka rabu. Amma duk da haka, da ake batun sako ɗaliban Kurigan daga hannun Janbros, Dogo Gide ya taimaka wajen shiga tsakani kuma Janbros ya saurare shi,” inji shi.

Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato, ASP Ahmad Rufa’i, sai ya ce ba su da tabbaci.

“Da na ga hoton na yawo, sai na bincika, inda har zuwa yanzu ba mu samu wani tabbacin cewa ya mutu a wani asibiti a Sakkwato ba.

“Amma dai ko ma mene ne, komai zai fito fili kuma zan sake muku bayani nan gaba.”

Yanzu sai dai a jira sanarwar hukumomi a hukumance domin tabbatar da haƙiƙanin mutuwarsa ko akasin haka.

Wane ne Dogo Gide?

Dogo Gide wani kasurgumin ɗan bindiga da ya daɗe yana sheƙe ayarsa, kuma asalin sunansa Abdullahi Abubakar.

A watan Agustan bara ne ya fito ya ɗauki alhakin ɓaro jirgin saman sojojin Najeriya, wanda ya yi sanadiyar kashe sojoji da dama.

Asalinsa yaron fitaccen ɗan bindiga Buharin Daji ne, wanda za a iya cewa shi ne farkon gawurtaccen ɗan bindiga.

Dogo Gide ne ya kashe Buharin Daji a wata rigima da ta kaure a tsakaninsu a Jihar Zamfara, wanda a lokacin aka riƙa murna, ana tunanin tunda an kashe Buharin Daji, harkar ta ƙare.

Dogo Gide shi ne ya sace ɗaliban makarantar Yauri, da sauran manyan harkokin satar ɗalibai da sojoji da ma’aikata.

Kusan za a iya cewa shi ne ya buɗe kofar satar ɗaliban makaranta da ma’aikata maimakon satar mutanen gari kawai domin karɓar kuɗin fansa mai yawa.

Ya daɗe yana addabar jihohin Neja, inda ya fi zama da Kaduna da Zamfara da Sakkwato.

Hoton da ake yadawa

Aminiya ta bi diddigin hoton da ake yadawa, inda alamu suka nuna cewa hoton ba ya kama da sanannen hoton Dogo Gide da aka sani.

Fitaccen mai rubutu a shafin Facebook, Malam Yakubu Musa ya wallafa cewa, “In dai wannan shi ne Dogo Gide ɗin to mai rawanin ba shi ba ne. Ko kama ba su yi ba. Tsinin hanci da faɗin hanci.”

Wani mai suna Abdullahi Habib ya rubuta cewa, “Don Allah kafin mutane su fara yaɗa wani abu su riƙa bincike. Ina ta ganin wannan hoton cewa shi ne Dogo Gide da aka kashe. Ina so mutane su yi watsi da wannan magana. Ba Dogo Gide ba ne wannan. Wannan sunansa Ɗan Asabe, wanda aka fi sani da Sabebe.

“Dan Unguwar Tudun Nupawa ne a nan Kaduna, yana sana’ar gwangwan a Legas kuma tsohon ɗan kwallon Lambu United ne.

“Kwanaki auran shi ya taso har ya dawo Allah Ya jarabce shi da rashin lafiya, ya daɗe yana jinya da ya samu sauki ya koma Legas inda ya yi hatsari a bodar Seme kimanin mako biyu da suka gabata. Kuma shi Dogo Gide ai an ce harbin shi aka yi, Allah Ya jikan shi Ya gafarta masa.”

Hoton Dan Asabe da rigar kwallo da gawarsa a gefe
Hoton Dan Asabe da rigar kwallo da gawarsa a gefe