✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shin DSS ce ta azabtar da direban Buhari har ya mutu?

Hukumar ta ce ko sau daya ba ta taba tsare direban Buhari ba

Hukumar DSS ta musanta zargin da ake yi mata na tsarewa tare da azabtar da tsohon direban Shugaba Muhammadu Buhari mai suna Sa’idu Afaka.

Mutuwar tsohon direban a ranar Talata ta janyo rudani, inda wasu kafofin yada labarai na kasar ke zargin cewa Hukumar DSS ce ta azabtar da shi wanda hakan ne ya yi sanadiyar ajalinsa.

Sai dai cikin wata sanarwa da kakakin Hukumar, Peter Afunanya ya fitar ranar Alhamis, ta musanta rahotannin da cewa kanzon kurege ne.

A cewar Peter, ba wani dalili da ya taba sanya Hukumar kama direban ballantana har ta kai ga tsarewa ko azabtar da shi.

Ya shawarci al’umma da suka rika watsi da labaran da ba su da tushe ballantana kuma wata madogara ta gaskiya.

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Talata, 6 ga watan Afrilu, 2021, mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya sanar da rasuwar Sa’idu Afaka.

Sanarwar da hadimin Shugaban kasar ya fitar ta ce Sa’idu ya rasu ne bayan wata jinya mai tsawo da ya yi a Asibitin Fadar Gwamnati da ke Abuja.

Garba Shehu ya ce ubangidansa yana mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin da kuma Gwamnati da al’ummar Jihar Kaduna da ta kasance cibiyarsa.