Najeriya A Yau: Shin Najeriya kasa ce mai ’yanci? | Aminiya

Najeriya A Yau: Shin Najeriya kasa ce mai ’yanci?

    Halima Djimrao

Domin sauke shirin latsa nan.

Bayan shekara 61 da samun ’yancin Najeriya, wasu ’yan kasar na bayyana shakku game da zaman kasar tasu mai cikakken ’yanci.

A gefe guda kuma al’ummomin duniya sai taya kasar murna suke ta yi game zagayowar ranar samun ’yancin kan nata daga turawan mulkin mallaka.

Shirin Najeriya ya gayyato masana kuma sun yi bayani dalla-dalla game irin ’yancin na Najeriya, wadda ta yi bikin zagayowar ranar ’yancin nata a ranar 1 ga watan Oktoba, 2021.

A yi sauraro lafiya.