✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin saka finafinai a YouTube zai riƙe Kannywood?

Kusan za a iya cewa yanzu Kannywood ta fara komawa YouTube baki dayanta.

A hankali a hankali kusan za a iya cewa yanzu Kannywood ta fara komawa YouTube baki dayanta.

Tun bayan rugujewar kasuwar CD, sai masana’antar ta fara durkushewa, inda masu shirya finafinai da dama suka koma wata sana’ar.

Ana cikin haka ne aka fara batun bude sinima a shekarar 2015, inda aka yi tunanin an samu mafita a kan matsalar da tabarbarewar tattalin arzikin masana’antar.

Sai dai binciken Aminiya ya gano cewa sinimonin suna dai dan tabawa ne kawai, domin ba a samun kudaden da aka zata za a samu.

Binciken Aminiya ya gano cewa fim din da ya fi tara kudi a sinimar Kano, shi ne fim din Aisha na forodusa Abubakar Bashir Maishadda, wanda darakta Hafiz Bello ya bada umarni.

An samu kudi Naira 5,641,000 a fim, wanda idan aka kwatanta da kasuwar CD, za a ga cewa ba komai ba ne wannan.

Kwatsam ana ci gaba da lallabawa da sinimar, sai kuma annobar coronavirus ta zo, inda aka hana taruka, ciki kuwa har da zuwa sinima kallon fim.

Wannan ya sa furodusoshi da dama suka fara tunanin komawa bangaren da a da can ba su cika damuwa da shi. Wato bangaren nuna fim a intanet wato tashar YouTube din.

A YouTube, abin da ake bukata kawai shi ne mutum ya bude tasharsa, sannan idan ya yi fim, ya dora a tashar, idan mutane suka kalla kuma su mahukunta YouTube su biya shi.

Wannan ya fi sauki da saurin isa ga mutane. Tun kafin Coronavirus din, dama can akwai finafinai masu dogon zango irinsu Gidan Zango na kamfanin White Birds Movie, Kaduna da sauransu.

Dukkan manyan forodusoshin Kannywood sun koma YouTube Za a iya cewa nasarar da fim din Izzar so ya samu ce ta bude kofar komawa YouTube da finafinai a Kannywood.

Kafin Izzar so, akwai finafinai irin su Hamar wanda ake nunawa a tashar AWA 24 Entertainment a YouTube da sauransu sun riga Izzar so.

Shi kansa jarumi Abale da ake ganin ya fi kowa cin moriyar YouTube a fim din Haram ne ya fito da sunan Ojo, inda ya taka rawa irin wadda ya taka a A duniya.

A yanzu za a iya cewa manyan forodusohin Kannywood su ne Abubakar Bashir Maishadda da Abdul Amart Maikwashewa da Naziru Dan Hajiya da Alhaji Sheshe da 2 Effects na su Sani Danja da Yakubu Mohammed da sauransu.

Kusan dukkan manyan masu shirya finafinan sun koma YouTube da kuma Arewa24, inda yanzu haka Maishadda yake daukar sabon shirinsa mai dogon zango mai suna Gidan Sarauta, bayan fim dinsa na Dan jarida da ake nunawa a Arewa24 da YouTube.

Shi ma Abdul Amart Maikwashewa ya yi fim din Manyan Mata mai dogon zango sannan yanzu haka yake daukar shirin Zafin nema.

Hakazalika, shi ma Alhaji Sheshe ya dauki shiri mai dogon zango na Mafita, sannan Naziru Dan Hajiya ya yi fim din Ke duniya da dai sauransu.

Wadannan finafinai duk da cewa ana nuna wasunsu a tashar Arewa24, dukansu ana nunawa a YouTube, inda ko dai a saka biyun, ko kuma a saka a YouTube kawai.

A nasa bangaren, Darakta Ali Nuhu yana yin Alaka, sannan ga Labarina na Aminu Saira.

Saboda rashin samun riba a sinima, fim din Bin Ali na Abdul Amart da aka yi domin haskawa a sinima, a karshe yanka fim din ya yi ya saka a YouTube.

Sai dai a wata tattaunawa da Aminiya, Naziru Dan Hajiya ya bayyana cewa suna bukatar samun wasu hanyoyin samar da kudade ga masana’antar ba ta’allaka da YouTube na kadai.

Sai dai wani abu da ake jifar Kannywood shi ne yadda har yanzu ba a samu fim din da aka fara aka gama ba.

Har yanzu ana ci gaba da nuna fim din Dadin Kowa na Arewa24, wanda yanzu an yi shekaru ana yi Shi ma Izzar so, duk da korafin da wasu suka yi na bukatar a kammala shirin, har yanzu ana ci gaba da yin sa.

A tattaunawar Ali Nuhu da Hadiza Gabon, ya bayyana cewa suna fata finafinan Kannywood za su samu shiga manhajar Netflix, kasancewar a can din ne za su samu makudan kudade su inganta masana’antar.

A cewarsa, a da can shi da wasu masu shirya finafinai a masana’antar sun tura finafinansu, amma ba su samu karbuwa ba, inda ya ce amma kasancewar an samu kishiyar Netflix din, wato Amazons, kuma sun nuna sha’awar finafinan Hausa, yana tunanin hakan zai sa Netflix din ma su sauko.

Sai dai ya yi kira gare su da akwai bukatar su kara inganta finafinan nasu, inda ya ce ba su da matsalar jarumai da labara, sai dai dan bukatar kara habaka bangaren kayan aiki da suke da shi.