✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban hukumar wasanni ta Jihar Gombe ya ajiye aiki

Shugaban Hukumar Wasannin ta Jihar Gombe, Hamza Adamu Soye, ya ajiye aiki.

Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Gombe, Malam Hamza Adamu Soye, ya yi murabu daga mukaminsa.

Ajiye aikin nasa na dauke ne a wata takarda mai dauke da sa hannunsa da ya fitar ta shafinsa na sada zumunta a ranar Talata, 15 ga watan Fabrairu, 2022.

Adamu Soye, ya gode wa Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya bisa damar da ya ba shi ya yi aiki wa jiharsa na wani lokaci a matsayin shugaban hukumar wasanni.

Sai dai bai bayyana dalilinsa na ajiye aikin ba, kuma binciken da wakilinmu ya gudanar bai kai ga ganowa ba.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakinsa, inda ya nemi shi a waya, amm bai dauka ba.