✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugaban Jam’iyyar Labour na Kasa ya rasu

Za a yi jana’izar Abdulkadir Abdulsalam da karfe 5 na yammacin Talata.

Shugaban Jam’iyyar Labour (Labour Party) na Kasa, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam ya rasu.

Sakataren Gamayyar Kwamitin ba wa Jam’iyyu Shawara (IPAC), Manjo Agbo ne ya shaida wa wakilinmu rasuwar, ta rubutaccen sakon.

Shugaban IPAC Dakta Yunusa Tanko, ma ya tabbatar da rasuwar ta sakon waya da ya aike wa wakilin namu.

A lokacin da ya aike wa wakilin namu sako ya tabbatar da cewa ana shirye-shiryen jana’izar mamacin ne.

Rahotanni sun ce za a yi jana’izar mamacin ne a Babban Masallacin Minna da ke Jihar Neja da misalin karfe 5 na yammacin ranar Talata.

Har wa yau, Tanko ya bukaci ’yan uwasu ’yan gwagwarmaya su halarci jana’izar.