✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Rikon APC Buni ya ziyarci Buhari a Landan

Buhari ya amince Mai Mala Buni ya ci gaba da jagorancin APC.

Shugaban Kwamitin Riko na Jam’iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari a Landan.

A halin yanzu shugaba Buhari yana ziyara a Birtaniya ne domin ganin likitansa.

Buhari ya kuma amince Mai Mala Buni ya ci gaba da jagorancin APC a matsayinsa na shugaban kwamitin riko na jam’iyyar, kamar yadda Hon Faruk Adamu Aliyu jigo a jam’iyyar APC ya shaida wa BBC.

Ya ce Buhari ya amince Mai Mala Buni ya ci gaba da aikin jagorancin babban taron jam’iyyar da ake shirin gudanarwa a ranar 26 ga watan Janairu, duk da wani umarnin kotu da ya ce a dakatar da taron.

Buni da Buhari da Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu a Landan

Shugabancin APC ya shiga rudani ne a karshen watan Fabarairu tun bayan da Gwamnan Neja Abubaukar Sani Bello ya ayyana kansa a matsayinsa mai jagorancin kwamitin.

Daga baya kuma wata wasika ta bulla cewa Mai Mala ne ya ba shi riko saboda ya yi tafiya kasar waje don a duba lafiyarsa, bayan da Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta ce sam ba ta san wannan zancen ba.

Rikicin shugabanci a APC ya kara kamari ne tun bayan da wasu gwamnoni, ciki har da Nasir El-Rufai na Kaduna, suka ce Shugaba Muhammadu Buhari ne ya ba da umarnin a sauke Mai Mala Buni, wanda ya fara jagoranci tun watan Yuni na 2020.