✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji biyu sun shiga hannu kan zargin sata a Matatar Dangote

Ana ci gaba da bincike don gano da tabbatar da cikakken laifin sojojin da aka kama.

Rundunar Sojin Ƙasa ta Nijeriya ta sanar da bayyana damuwa kan zargin sata da ake yi wa wasu jami’anta biyu a Matatar Mai ta Dangote da ke Jihar Legas.

“Wannan aika-aika, wadda dakarun sa-kai da jami’an tsaro masu zaman kansu da ke aiki a matatar man suka daƙile, abu ne da ba za a amince da shi ba, kuma abin takaici ne matuƙa.

“Don haka ba ya wakiltar ɗa’a da ƙimar rundunar soji,” in ji sanarwar da mai magana da yawun rundunar Sojin Ƙasa na Nijeriya, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar a wannan ranar Laraba.

Ta ce tuni aka gano wadanda ake zargin kuma ana tsare da su a yanzu haka.

“Binciken farko ya bayyana cewa wani ɗan kwangila ne da aka bayyana sunansa da Mista Smart ya dauki hayar mutanen biyu, wanda ya yi ikirarin cewa yana so ne ya ƙwato wasu igiyoyin sulke na da ya bari a harabar matatar.

“Su sojoji ba su sani ba,da ɗan kwangilar ya gano za a samu matsala a lokacin da suke tunkrara wajen bincike na matatar, sai ya ɗauki uzuri ya fice daga motar ya bar su a wajen,” a cewar sanarwar.

Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike don gano da tabbatar da cikakken laifin sojojin da aka kama.

Kazalika ta ce an gano wayoyin da aka sace ɗin kuma ƙwace su.

Rundunar soji ta ce tana aiki kafada-da-kafada da hukumar gudanarwar Matatar Mai ta Dangote don tabbatar da cewa an yi cikakken bincike a kan “wannan mummunan lamari.”

“Rundunar soji na son tabbatar wa da jama’a cewa za a ɗauki matakan ladabtarwa da suka dace kan wadanda suka aikata laifin, saboda ba za ta lamunci irin wannan wani laifi a cikin ma’aikatanta ba,” ta ƙara da cewa.