✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun tarwatsa ‘yan bindiga a dazukan Kaduna

Dakarun Sojin Najeriya na rundunar tsaro ta Operation Thunder Strike sun ragargaji ‘yan bindiga tare da tarwatsa sansaninsu a dajin Kuyambana da ke Jihar Kaduna.…

Dakarun Sojin Najeriya na rundunar tsaro ta Operation Thunder Strike sun ragargaji ‘yan bindiga tare da tarwatsa sansaninsu a dajin Kuyambana da ke Jihar Kaduna.

Daraktan samar da bayanai na rundunar tsaro, Manjo Janar John Enenche ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja.

Ya ce sojojin sun dandana wa ‘yan bindigar kudarsu da jerin hare-haren na dajin Kuymbana.

Manjo Janar Enenche ya ce an kai hare-haren ne ranar Alhamis bayan samun muhimman bayanai da suka kai ga gano maboyar ‘yan ta’addan da kuma wurin taronsu.

Ya kara da cewa sun kuma yi amfani da jiragen rundunar sojin saman Najeriya wajen kai wasu daga cikin hare-haren.