✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojoji sun yi wa ’yan bindiga ruwan wuta a Kaduna

Dakaru sun tsallaka Kogin Kaduna inda suka rika musayar wuta da ’yan bindiga.

Dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar kashe ’yan bindiga da dama a wani samame da suka kai yankin Galbi da ke Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

A cewar Aruwan, rundunar Operation Forest Sanity tare da hadin gwiwar sojojin sama ne suka far wa matattarar ’yan bindiga a yankin na Galbi.

Duk da cewa kwamishinan bai bayyana adadin ’yan bindigan da aka kashe ba, amma ya ce dakarun sun samu nasarar kwace bindigogi masu sarrafa kan su guda biyu da kuma AK47 guda uku da babura bakwai.

Ya bayyana cewa, tun da farko dakarun sun tsallaka Kogin Kaduna inda suka rika musayar wuta da ’yan bindigar, wanda a dalilin haka ne suka kashe da dama daga cikinsu.

Sanarwar ta ce Gwamnatin Kaduna ta gode wa sojojin kasa da na sama da ’yan sanda da jami’an tattara bayanan sirri da ’yan bijilanti da wadanda suka taimaka wurin samun wannan nasara.

Aruwan ya kuma bukaci jami’an tsaron da su kara kaimi wajen fatattakar ‘yan ta’addan da suka samu mafaka a wasu dazukan da sauran maboyar ’yan bindigar da aka gano a fadin jihar.