✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojojin Habasha sun kwace birnin yankin Tigray

Sojojin Habasha da Eritrea sun kwace birnin Shire mai matukar da ke yankin Tigray daga ’yan tawaye.

Sojojin Habasha tare da takwarorinsu na Eritrean sun kwace birnin Shire mai matukar muhimmanci a Arewa maso Yammacin Tigray daga hannun ’yan tawaye.

’Yan tawaye Tigray sun ce a safiyar Talata dakarun gwamnati, “sun kwace wasu yankuna ciki har da Shire, amma mun tsaya sai bayan ranmu.”

’Yan tawayen sun ce sojojin sun kutsa garin Shire na ranar Litinin “suna ragargaza babu kakkautawa.”

Zargin na zuwa ne washegarin da gwamnatin Habasha ta lashi takokin kwace filin jirgi da sauran wurare da ke yankin Tigray.

An dade ana gwabza kazamin fada tsakanin sojoin kasashen Habasha da Eritrea a bangare guda, da kuma ’yan tawaye Tigray a daya bangaren, wanda hakan ya haifar da damuwa a tsakanin kasashe da hukumomin duniya.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce ba za a iya tantance ikirarin ’yan tawayen game da halin da ake ciki a yankin ba, saboda an katse layukan sadarwa kuma an hana ’yan jarida aiki a yankin.

Bayan kazancewar rikicin, a ranar Litinin, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi gargadin cewa idan ba a yi taka-tsantsan ba, rikicin na Habasha “na iya wuce duk yadda ake zato”.

Bayanin nasa na zuwa ne bayan a ranar Lahadi, kungiyar Tarayyar Afirka ta yi kira a a tsagaita wuta ba tare da wani sharadi ba tsakanin bangarorin da suka shafe kusan shekara biyu suna gwabza yaki.