✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa 9 a rana guda

Daga cikin mutanen har da wata tsohuwa

A wani hari mafi muni tun lokacin da Isra’ila ta kaddamar da luguden wuta a karshen shekarar da ta gabata kan Falasdinawa, sojojinta sun kashe mutum tara a rana guda a Gabar Yammacin Kogin Jordan.

Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta ce akalla wasu mutum 20 kuma sun jikkata daga harsasan harbin da aka yi musu a harin da Isra’ila ta kai kan wani sansanin Falasdinawa da ke yankin Jenin ranar Alhamis.

Falasdinawan sun bayyana harin a matsayin kisan kiyashi. Sun kuma ce yanzu haka, hudu daga cikin wadanda aka harba din na cikin hali rai kwakwai, mutu kwakwai.

Daga cikin mutanen da aka kashe dai har da wata tsohuwa mai suna Magda Obaid, kamar yadda hukumomin asibitin Jenin suka tabbatar.

Sojojin na Isra’ila dai wadanda suka janye daga yankin na Jenin bayan aikata kashe-kashen dai sun ce suna bibiyar rahoton kisan matar.

A wani labarin kuma, wata rundunar tsaro ta jam’iyyar Fatah ta Falasdinawa da ke gadin masallacin birnin Kudus, ta ce daga cikin wadanda Isra’ilan ta kashe har da daya daga cikin mayakanta, Izz al-Din Salahat.

Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinun kuma ta ce shi ma wani matashi mai shekara 24 mai suna Saeb Azriqi, ya riga mu gidan gaskiya a asbiti.

Ma’aikatar ta kuma zargi Isra’ila da tattare motocin daukar marasa lafiya da ke kokarin kai wadanda aka jikkata zuwa asibiti.