✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojojin Mali sun kashe ’yan tawaye sama da 200

Ana dai fargabar daga cikin mutanen da aka kashe har da fararen hula

Sojojin kasar Mali sun ce sun kashe mayakan ’yan tawaye 203 a yankin Mora da ke tsakiyar kasar.

Sai dai dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar sun yi zargin cewa daga cikin wadanda aka kashe din har da fararen hula, lamarin da ya sa ake zargin an take hakkin bil-Adama.

Sojojin dai a ranar Juma’a sun ce sun hallaka mayakan ne yayin wasu jerin hare-hare da suka kai yankin na Mora da ke tsakiyar kasar, tsakanin 23 da 31 ga watan Maris din 2022.

Bugu da kari, sojojin sun kuma ce sun kama mutum 51 tare da kwace tarin makamai daga hannunsu.

Sanarwar sojojin dai na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni da dama musamman a kafafen sada zumunta na kasar suka yi zargin an kashe fararen hula a yankin.

Sai dai Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ce ba za a iya tantance gaskiyar ikirarin sojoji ba, ko kuma rahotannin kafafen sada zumuntar.

Wahalar shigar da ake samu zuwa yankunan da ke fama da rikice-rikice a kasar Mali dai da kuma karancin hanyoyin tabbatar da alkaluman, ya sa yana da wahala a tantance gaskiyar abin da ke faruwa a yankin.

Mali dai na zargin yankin da cewa yana karkashin kulawar kungiyar da ke da alaka da Alka’ida da ISIS, inda take ta kokarin ganin ya kwato iko da shi.