✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon na hannun daman Buhari Solomon Dalung ya fice daga APC

Ya ce ya fice daga jam'iyyar APC ne saboda rashin dimokuradiyyar cikin gida.

Tsohon Ministan Wasanni kuma na hannun daman Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Solomon Dalung, ya fice daga jam’iyya mai mulki ta APC.

Dalung ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar ne ta wata takarda da ya shugaban mazabarsa ta  Sabongida da ke Karamar Hukumar Langtang ta Jihar Filato ranar Litinin, 18 ga Afrilu, 2022.

Tsohon ministan ya bayyana cewa ya rashin dimokuradiyyar cikin gida ta na, “Nake sanar da ku cewa daga yau na fice daga jam’iyya.

“Sanin kowa ne cewa abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar a bayan nan sun saba da tsarina da ya sa ni shiga jam’iyyar.

“Tabbas dimokuradiyyar cikin gida ginshiki ne da dorewar dimokuradiyya ta gaskiya, wanda muddin babu shi to babu amfanin shiga siyasa.”