✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ta yaya ba zan shiga damuwa ba?

Da yawa suna zargin Baba Buhari da gazawa wajen kare rayuka da dukiyoyi.

Magana ce a kan Shugaba Muhammadu Buhari, mutumin da Allah Ya nufa da farin jinin da ba a taba samun dan siyasa irinsa ya samu ba a tarihin Najeriya.

Kaunar da aka yi masa har yaduwa ta yi zuwa duk wani wanda aka hango tsaye a inda Shugaba Buhari yake.

Dauki misali da ni Biyora, hango ni aka yi ina sa bidiyon wuraren da Shugaba Buhari yake zuwa yawon kamfen a shekarar 2014 kuma aka ga ina rubutun karfafa wa masu kaunar Buhari gwiwa, sai nan da nan al’umma suka rika bibiya ta saboda Buhari, wanda hakan ya zama babbar nasara ga rayuwata.

To me ya sa na damu?

Ganin yadda aka wayi gari Muhammadu Buhari da al’umma suka mutumta mu saboda shi, yanzu ya zama abin zolaya, har ma idan aka ce ya fitar da sanarwa a matsayinsa na Shugaban Kasa, sai ka ga da kyar ake samun mutane kalilan da suke amincewa da abin da ya ce.

Shugaba Buharin da ba ka isa ka yi gangancin furta bakar magana gare shi ba, koda kuwa a cikin gidanku ne kafin ya zama Shugaban Kasa.

Na tabbata da a ce Shugaba Buhari ya samu nasarar samar da cikakken tsaro tare da yalwatar arziki a Najeriya da mu kanmu da muke rubutu a kansa, da mun samu karin daukaka da kwarjini, ta dole ba don muna so ba.

Sai mu yi kwana 30 ba tare da mun yi rubutun da ya shafe shi ba a yanzu, duk a tsoron da muke na kada wadansu su zage shi su zage mu tare da bakaken maganganu.

Na san siyasa ake, koda a ce ya dawo da Naira daidai da Dalar Amurka, dole a samu masu adawa, to amma da ba za su yi yawa ba, kamar yadda a yanzu bayan masu adawa har da masu kiyayya, saboda da yawa suna zargin Baba Buhari da gazawa wajen kare rayuka da dukiyoyi.

Tsakani da Allah ban so haka ba, kuma shi ya sa na kasa daina yi wa Shugaba Buhari addu’ar samun damar yin ayyukan da za su dawo masa da kwarjini da mutuncin da mu ma zai ci gaba da shafarmu, Allah Buwayi gagara misali muke roko Ya taimaki Shugaba Muhammadu Buhari a ragowar shekarun da suka rage masa, komai mai sauki ne gare Ka Allah.

A zahiri akwai damuwa ba za mu so a ce Shugaba Buhari ya kammala mulkin al’umma na yi masa irin kallon da suke masa a yanzu ba. Tabbas dole in damu.

Fitaccen marubuci a kafafofin sadarwa Rabi’u Biyora ne ya rubuta wannan mukala a shafinsa na facebook.